1 SRK Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu. BSB BSB: Paul, an apostle—sent not from men nor by man, but by Jesus Christ and God the Father, who raised Him from the dead—
2 SRK Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan, Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya. BSB BSB: and all the brothers with me, To the churches of Galatia:
3 SRK Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. BSB BSB: Grace and peace to you from God our Father and the Lord Jesus Christ,
4 SRK Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu, BSB BSB: who gave Himself for our sins to rescue us from the present evil age, according to the will of our God and Father,
5 SRK a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. BSB BSB: to whom be glory forever and ever. Amen.
7 SRK wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi. BSB BSB: which is not even a gospel. Evidently some people are troubling you and trying to distort the gospel of Christ.
9 SRK Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada! BSB BSB: As we have said before, so now I say again: If anyone is preaching to you a gospel contrary to the one you received, let him be under a curse!
10 SRK Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba. BSB BSB: Am I now seeking the approval of men, or of God? Or am I striving to please men? If I were still trying to please men, I would not be a servant of Christ.
11 SRK Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. BSB BSB: For I want you to know, brothers, that the gospel I preached was not devised by man.
12 SRK Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne. BSB BSB: I did not receive it from any man, nor was I taught it; rather, I received it by revelation from Jesus Christ.
14 SRK Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina. BSB BSB: I was advancing in Judaism beyond many of my contemporaries and was extremely zealous for the traditions of my fathers.
15 SRK Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi BSB BSB: But when God, who set me apart from my mother’s womb and called me by His grace, was pleased
16 SRK yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba. BSB BSB: to reveal His Son in me so that I might preach Him among the Gentiles, I did not rush to consult with flesh and blood,
17 SRK Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus. BSB BSB: nor did I go up to Jerusalem to the apostles who came before me, but I went into Arabia and later returned to Damascus.
20 SRK Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne. BSB BSB: I assure you before God that what I am writing to you is no lie.
21 SRK Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya. BSB BSB: Later I went to the regions of Syria and Cilicia.
22 SRK Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna. BSB BSB: I was personally unknown, however, to the churches of Judea that are in Christ.
23 SRK Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.” BSB BSB: They only heard the account: “The man who formerly persecuted us is now preaching the faith he once tried to destroy.”
24 SRK Sai suka yabi Allah saboda ni. BSB BSB: And they glorified God because of me.
Select verses for actions: Enter goes to them and Escape comes back.