2 SRK kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. BSB BSB: just as they were handed down to us by the initial eyewitnesses and servants of the word.
3 SRK Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, BSB BSB: Therefore, having carefully investigated everything from the beginning, it seemed good also to me to write an orderly account for you, most excellent Theophilus,
4 SRK don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai. BSB BSB: so that you may know the certainty of the things you have been taught.
6 SRK Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. BSB BSB: Both of them were righteous in the sight of God, walking blamelessly in all the commandments and decrees of the Lord.
7 SRK Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa. BSB BSB: But they had no children, because Elizabeth was barren, and they were both well along in years.
8 SRK Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah, BSB BSB: One day while Zechariah’s division was on duty and he was serving as priest before God,
9 SRK sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare. BSB BSB: he was chosen by lot, according to the custom of the priesthood, to enter the temple of the Lord and burn incense.
10 SRK Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a. BSB BSB: And at the hour of the incense offering, the whole congregation was praying outside.
11 SRK Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare. BSB BSB: Just then an angel of the Lord appeared to Zechariah, standing at the right side of the altar of incense.
12 SRK Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. BSB BSB: When Zechariah saw him, he was startled and gripped with fear.
13 SRK Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. BSB BSB: But the angel said to him, “Do not be afraid, Zechariah, because your prayer has been heard. Your wife Elizabeth will bear you a son, and you are to give him the name John.
14 SRK Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, BSB BSB: He will be a joy and delight to you, and many will rejoice at his birth,
15 SRK gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa. BSB BSB: for he will be great in the sight of the Lord. He shall never take wine or strong drink, and he will be filled with the Holy Spirit even from his mother’s womb.
16 SRK Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu. BSB BSB: Many of the sons of Israel he will turn back to the Lord their God.
18 SRK Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.” BSB BSB: “How can I be sure of this?” Zechariah asked the angel. “I am an old man, and my wife is well along in years.”
19 SRK Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. BSB BSB: “I am Gabriel,” replied the angel. “I stand in the presence of God, and I have been sent to speak to you and to bring you this good news.
20 SRK Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.” BSB BSB: And now you will be silent and unable to speak until the day this comes to pass, because you did not believe my words, which will be fulfilled at their proper time.”
21 SRK Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. BSB BSB: Meanwhile, the people were waiting for Zechariah and wondering why he took so long in the temple.
22 SRK Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana. BSB BSB: When he came out and was unable to speak to them, they realized he had seen a vision in the temple. He kept making signs to them but remained unable to speak.
23 SRK Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. BSB BSB: And when the days of his service were complete, he returned home.
24 SRK Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. BSB BSB: After these days, his wife Elizabeth became pregnant and for five months remained in seclusion. She declared,
25 SRK Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.” BSB BSB: “The Lord has done this for me. In these days He has shown me favor and taken away my disgrace among the people.”
27 SRK gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. BSB BSB: to a virgin pledged in marriage to a man named Joseph, who was of the house of David. And the virgin’s name was Mary.
28 SRK Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.” BSB BSB: The angel appeared to her and said, “Greetings, you who are highly favored! The Lord is with you.”
29 SRK Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka? BSB BSB: Mary was greatly troubled at his words and wondered what kind of greeting this might be.
30 SRK Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. BSB BSB: So the angel told her, “Do not be afraid, Mary, for you have found favor with God.
31 SRK Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. BSB BSB: Behold, you will conceive and give birth to a son, and you are to give Him the name Jesus.
32 SRK Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, BSB BSB: He will be great and will be called the Son of the Most High. The Lord God will give Him the throne of His father David,
33 SRK zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.” BSB BSB: and He will reign over the house of Jacob forever. His kingdom will never end!”
35 SRK Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. BSB BSB: The angel replied, “The Holy Spirit will come upon you, and the power of the Most High will overshadow you. So the Holy One to be born will be called the Son of God.
36 SRK ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. BSB BSB: Look, even Elizabeth your relative has conceived a son in her old age, and she who was called barren is in her sixth month.
37 SRK Gama ba abin da zai gagari Allah.” BSB BSB: For no word from God will ever fail.”
39 SRK A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, BSB BSB: In those days Mary got ready and hurried to a town in the hill country of Judah,
40 SRK inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. BSB BSB: where she entered the home of Zechariah and greeted Elizabeth.
41 SRK Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. BSB BSB: When Elizabeth heard Mary’s greeting, the baby leaped in her womb, and Elizabeth was filled with the Holy Spirit.
42 SRK Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! BSB BSB: In a loud voice she exclaimed, “Blessed are you among women, and blessed is the fruit of your womb!
43 SRK Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? BSB BSB: And why am I so honored, that the mother of my Lord should come to me?
44 SRK Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. BSB BSB: For as soon as the sound of your greeting reached my ears, the baby in my womb leaped for joy.
45 SRK Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!” BSB BSB: Blessed is she who has believed that the Lord’s word to her will be fulfilled.”
47 SRK ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona, BSB BSB: and my spirit rejoices in God my Savior!
49 SRK gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne. BSB BSB: For the Mighty One has done great things for me. Holy is His name.
50 SRK Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani. BSB BSB: His mercy extends to those who fear Him, from generation to generation.
51 SRK Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu. BSB BSB: He has performed mighty deeds with His arm; He has scattered those who are proud in the thoughts of their hearts.
52 SRK Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu. BSB BSB: He has brought down rulers from their thrones, but has exalted the humble.
53 SRK Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi. BSB BSB: He has filled the hungry with good things, but has sent the rich away empty.
54 SRK Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai BSB BSB: He has helped His servant Israel, remembering to be merciful,
55 SRK ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.” BSB BSB: as He promised to our fathers, to Abraham and his descendants forever.”
56 SRK Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida. BSB BSB: Mary stayed with Elizabeth for about three months and then returned home.
57 SRK Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. BSB BSB: When the time came for Elizabeth to have her child, she gave birth to a son.
58 SRK Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki. BSB BSB: Her neighbors and relatives heard that the Lord had shown her great mercy, and they rejoiced with her.
59 SRK A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, BSB BSB: On the eighth day, when they came to circumcise the child, they were going to name him after his father Zechariah.
60 SRK amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” BSB BSB: But his mother replied, “No! He shall be called John.”
61 SRK Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.” BSB BSB: They said to her, “There is no one among your relatives who bears this name.”
62 SRK Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. BSB BSB: So they made signs to his father to find out what he wanted to name the child.
63 SRK Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. BSB BSB: Zechariah asked for a tablet and wrote, “His name is John.” And they were all amazed.
64 SRK Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. BSB BSB: Immediately Zechariah’s mouth was opened and his tongue was released, and he began to speak, praising God.
65 SRK Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. BSB BSB: All their neighbors were filled with awe, and people throughout the hill country of Judea were talking about these events.
66 SRK Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi. BSB BSB: And all who heard this wondered in their hearts and asked, “What then will this child become?” For the Lord’s hand was with him.
67 SRK Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce, BSB BSB: Then his father Zechariah was filled with the Holy Spirit and prophesied:
68 SRK “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa. BSB BSB: “Blessed be the Lord, the God of Israel, because He has visited and redeemed His people.
69 SRK Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda BSB BSB: He has raised up a horn of salvation for us in the house of His servant David,
70 SRK (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki), BSB BSB: as He spoke through His holy prophets, those of ages past,
71 SRK cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu BSB BSB: salvation from our enemies and from the hand of all who hate us,
72 SRK don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, BSB BSB: to show mercy to our fathers and to remember His holy covenant,
73 SRK rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim, BSB BSB: the oath He swore to our father Abraham, to grant us
74 SRK don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro, BSB BSB: deliverance from hostile hands, that we may serve Him without fear,
75 SRK cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu. BSB BSB: in holiness and righteousness before Him all the days of our lives.
76 SRK “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya, BSB BSB: And you, child, will be called a prophet of the Most High; for you will go on before the Lord to prepare the way for Him,
77 SRK don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu, BSB BSB: to give to His people the knowledge of salvation through the forgiveness of their sins,
78 SRK saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama, BSB BSB: because of the tender mercy of our God, by which the Dawn will visit us from on high,
79 SRK don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.” BSB BSB: to shine on those who live in darkness and in the shadow of death, to guide our feet into the path of peace.”
80 SRK Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila. BSB BSB: And the child grew and became strong in spirit; and he lived in the wilderness until the time of his public appearance to Israel.